Isa ga babban shafi
Yemen

An soma tattaunawar rikicin Yemen a Kuwait

An fara gudanar da zaman tattauna kawo karshan rikicin kasar Yemen a Kuwait karkashin inuwar Majalisar Dinkin Duniya, inda aka bukaci hadin kan wakilan bangarorin ‘yan tawaye kasar da na Gwanatin domin cimma matsayar sake gina kasar da yaki ya daidaita watanni 13 yanzu.

Mohammed Abdul-Salam, Shugaban wakilan 'Yan Tawayen Yemen a tattaunawar sulhu da gwamnati a Kuwait
Mohammed Abdul-Salam, Shugaban wakilan 'Yan Tawayen Yemen a tattaunawar sulhu da gwamnati a Kuwait REUTERS
Talla

Ministan harakokin wajen Kuwait Sheikh Sabah al-Khaled da ke bude taron ya bayyana tattaunawar a matsayin irinta na farko a tarihi da ake fatan kawo karshen zub da jini a kasar

Tuni dai tawagar ‘yan tawayen Huthi da ke goyon bayan tsohon shugaba Ali Abdullah Saleh suka isa kasar domin shiga tattaunawar.

Manzon Majalisar Dinkin Duniya na musamman Ismail Ould Cheikh Ahmed ya bukaci bangarorin da ke rikici da juna da su yi aiki tare wajen cimma yarjejeniyar da zai sake farfado da kasar.

Daga cikin bukatun ‘yan tawayen kasar dai akwai kawo karshan hare-haren kasashen kawance na larabawa a kasar da kuma takukuman da aka kakabawa Abdallah Saleh.

Sama da mutane 6,400 aka kashe a yakin kasar, yayin da wasu akalla miliyan 2.8 suka rasa muhallinsu tun bayan lokacin da Saudiya da kawayenta suka zafafa hare-hare a watan maris din bara kan ‘yan tawayen Huthi da Iran ke marawa baya, masu iko da birane kasar da dama ciki har da birni Sanaa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.