Isa ga babban shafi
Isra'ila-Falesdinu

Isra'ila na ci gaba da gina gidaje a yankunan Falesdinawa

Kungiyar wanzar da zaman lafiya dake sa ido kan halin da ake ciki a Isra’ila da ake kira ‘’Peace Now’’ tace gwamnatin kasar ta fara gina gidajen yan kama wuri zauna 1,800 a Gabar Yamma da kogin Jordan.Kungiyar tace adadin gidajen zai kai 3,100 da Israila ta gina a Yankunan Falasdinawa a shekarar 2014. 

Wasu filayen da Isra'ila ta karbe daga Falesdinu
Wasu filayen da Isra'ila ta karbe daga Falesdinu
Talla

Kungiyar tace yanzu haka Yahudawa 380,000 ke zama a Yankunan Falasdinawa dake Gabar Yamma da kogin Jordan yayin da wasu 200,000 ke zama a Gabashin Birnin Kudus.
Isra'ila na ci gaba da keta yarjejeniyoyin ,dama tursasawa Falesdinawa duk da yake kasashen Duniya na fatar ganin an kawo karshen rikicin tsakanin Isra'ila da Falesdinu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.