Al Nusra ta yi watsi da matakin ‘Yan adawar Syria
Kungiyar al Nusra mai alaka da Mayakan Al Qaeda ta yi watsi da bukatun kungiyoyin ‘Yan tawayen Syria da suka amince a Saudiya su hau teburin tattaunawa da shugaban kasar Bashar al Assad.
Wallafawa ranar:
Shugaban kungiyar ta Al Nusra Abu Muhammed Al Jolani ne ya yi watsi matakin wanda ya danganta a matsayin tarko tare da zargin ‘Yan adawar da laifin cin amanar kasa.
Wannan dai na zuwa a yayin da sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry zai nufi Moscow domin tattaunawa da mahukuntan Rasha kan batun shawo kan rikicin Syria.
A ranar Alhamis ne kungiyoyin ‘Yan adawar Syria suka amince su hada kai domin tunkarar Shugaba Bashar Assad a teburin tattaunawa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu