'Yan adawar Syria za su tattauna da gwamnatin kasar
Kungiyoyin ‘yan adawar Syria sun amince da zaman tattaunawa da gwamnatin shugaba Bahsar al-Assad, sai dai sun dage kan matsayinsu cewa dole Assad ya mika mulki ga gwamnatin rikwan kwarya domin gudanar da sabon zabe a kasar.
Wallafawa ranar:
Bayan kammala taro irinsa na farko da Saudiya ta jagoranta kan sulhunta rikicin Syria da ‘yan adawar kasar, dukkanin bangarorin siyasar kasar da ke adawa da shugabancin Bashar al-assad sun yi na’am da zaman tattaunawar, sai dai suna kan bakarsu na ya sauka daga mulki.
Rahotanni sun ce, yayin wannan zaman akwai daya daga cikin kungiyon 'yan tawayen kasar, Ahrar al-Sham da ta fice daga zauran taron, yayin da wasu majiyoyi ke cewa ita ma ta sanya hannu kan wannan yarjejniya na zama da gwamantin Assad domin samo bakin zaren warware rikicin Syria.
Jami’an diflomasiyar kasashe 17 ne suka halarci wannan taro da nufin kawo karshen yakin Syria da ke nema shiga shekara ta 5.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu