Isa ga babban shafi
Afghanistan-Nato-Amurka

‘Yan Taliban sun raunana Shugaban kungiyar

Hukumomin kasar Afghanistan sun ce an raunana shugaban kungiyar Taliban Mullah Akhtar Mansour a wani rikicin cikin gida tsakanin su lokacin da suke gudanar da taron kwamnadodjin kungiyar. 

Yan kungiyar Talibans a kasar Afghanistan
Yan kungiyar Talibans a kasar Afghanistan
Talla

Sultan Faizi, mai magana yawun mataimakin shugaban kungiyar, yace wasu ya ‘an kungiyar biyar suka mutu a rikicin.
Watanni hudu kenan da nada Mansour a matsayin shugaban kungiyar.
 

A yan watani da suka gabata an samu barkewar rikici tsakanin bangarorin kungiyar mayakan Taliban da ke gaba da juna a kudancin lardin Zabul a kasar Afghanistan. Mayakan da dama ne aka ruwaito sun mutu a rikicin da ya barke tsakanin masu biyayya ga Mullah Akhtar Mansour da kuma mabiyan Mansoor Dadullah.

Jami’an tsaron Afghanistan sun ce tun a ranar Assabar ne rikicin ya barke, kuma rikicin ya sa an tsinci gawarwakin mutanen kabilar Hazaras da mayakan suka sace a watan Oktoba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.