Isa ga babban shafi
Yemen-Saudiya

An kashe mahalarta bikin daurin aure 131 a Yemen

Rahotanni daga Yemen sun ce a yanzu mutane 131 da suka hada da kanana yara da mata ne suka mutu a harin sama da Saudiya ta kai musu bisa kuskure, lokacin hallatar bikin daurin aure, harin da saudiya da kawayenta masu kai hare-haren sama a kasar suka musanta.

REUTERS/Mohamed al-Sayaghi
Talla

Tuni dai Sakatare Janar na Majalisar dinkin duniya Ban Ki-Moon ya yi allawadai da harin kan fararan hula, inda ya ce an take dokokin hakkin dan adam na kasa da kasa.

Mazauna yankin da lamarin ya auku sun tabbatar da cewa tabbas Saudiya da kawayenta da ke kaiwa mayakan Huthi hari ne suka kai wa taron bikin hari a bisa kuskure, a kauyen Wahijah da ke yankin kudu mai nisa na kasar bisa kuskure.

Saudiya da kawayenta magoya bayan gwamnatin Abdurabbu Mansur Hadi ta kwashe watanni tana kai hari a kan mayakan Houthi da Iran ke goyawa baya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.