Isa ga babban shafi
Yemen

ISIS ta kai hari masallacin Idi a Yemen

Kungiyar IS ta yi ikirarin kaddamar da harin kunar bakin waken da ya kashe mutane akalla 25 a wani masallacin dake birnin Sanaa na Kasar Yemen.

Mayakan IS sun sha kaddamar da hare hare a birnin Sanaa na Kasar Yemen.
Mayakan IS sun sha kaddamar da hare hare a birnin Sanaa na Kasar Yemen. REUTERS/Mohamed al-Sayaghi
Talla

Kungiyar ta IS dake da’awar kafa daular Islama a yankin gabas ta tsakiya ta sha kaddamar da hare a birnin Sanaa dake karkashin ikon 'Yan tawayen Houthi.

Harin Masallacin wanda ke kusa da Kwalejin horar da Jami’an 'Yan Sanda, na zuwa ne a daidai lokacin da Mayakan Houthi da magoya bayansu suka Masallacin domin gudanar da sallar Idi.

Shaidun gani da ido sun ce jim kadan da fashewar Bam din fako a cikin Masallacin, sai wani dan kunar bakin wake da ya tsaya a kofar shiga cikin Masallacin,shima ya kwance Bam din da ya yi dammara da shi, al-amarin da ya ruda masu ibada.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.