Isa ga babban shafi
Yemen-Saudi Arabia

Gwamnatin Yemen da ke gudun hijira a Saudiya ta dawo Aden

Gwamnatin kasar Yemen da ke gudun hijra a kasar Saudiya a yau laraba ta isa Aden gari mafi girma na biyu, bayan nasarar da aka samu na fatattakar mayakan Houthis da suka kwace ikon manyan garuruwan kasar a baya .

Shugaban Kasar Yemen Abderrabbu Mansur Hadi
Shugaban Kasar Yemen Abderrabbu Mansur Hadi REUTERS/Stringer
Talla

Kawo yanzu dai babu bayani na lokacin da shugaban kasar Abdourabuh Mansour Hadi zai isa Yemen daga Saudiya.

Tun watan Yulin da ya gabata ne dakarun kawance karkashin jagorancin kasar Saudiya suka soma aikin fatatakar mayakan Houthis daga Aden tare da kwace wasu manyan birane daga hannun su.
 

Sanarwar da mai magana da yawun gwamnatin ya Fitar Rajeh Badi ya shaida cewa yanzu haka gwamnatin ta bar bairnin Riyadh na Saudiya inda ta ke mafaka zuwa Aden.

Rahotan Majalisar Dinkin Duniya na cewa akalla mutane 4,900 suka rasa rayukansu sakamakon yaki a Yemen, yayin da wasu dubu 25 suka jikata daga watan Maris zuwa yanzu.

Kasar Yemen mai yawan al'umma Miliyan 25 sama da Mutane miliyan 21 yaki ya dai-dai ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.