Isa ga babban shafi
Yemen

ISIS ta kai hari a masallacin shi’a da ke Sanaa

Wani Jerin hare-haren kunar bakin wake da ta dau alhakin kai wa a birnin Sanaa na Kasar Yemen Kungiyar ISIS ta kashe mutane 28 tare da jikata wasu 75.Ko a baya ma Kungiyar ta kai irin wannan harin a masallacin Shi’a da ke kasar Kuwait da Saudi Arabia.

REUTERS/Khaled Abdullah
Talla

ISIS wacce a baya ma ta taba dau alhakin kai hari Sanaa, ta ce wani mutumin mai suna Qusai al-Sanaani ne ya ta da bam din a cikin masallacin, kana daga bisani ta dana wani bam din kuma a harabar masallacin dai-dai inda ladani masallacin ke ajiye motar sa.

A wani sako da ta aike shafin Twitta Kungiyar ta ce ta kai har ne a matsayin ramuwar gayyar laifukan da Shi’a ke aikatawa a Yemen.

Wannan harin dai na zuwa ne, yayin da wasu rahotanni ke cewa wani harin bindiga ya hallaka ma'aikatan kungiyar agaji ta Red Cross 2 a hanyar su ta komawa Sanaa daga birnin Saada.

A cewar mai magana da yawun kungiyar a Yemen Rima Kamal an kashe Jami'an ne a cikin motar Red Cross, bayan dan bindiga ya yi kokarin tsayar da su a lardin Amran wanda 'yan tawayen Huthi ke iko da shi tun a bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.