Isa ga babban shafi
Yemen

Gwamnatin Yemen ta fasa shiga tattaunawar sulhu

Gwamnatin kasar Yemen ta ce ta fasa halartar zaman tattaunawa tsakaninta da ‘yan tawayen Huthi inda ta bukaci ‘yan tawayen da su soma amincewa da kudurin Majalisar Dinkin Duniya na janyewa daga garuruwan da yanzu haka ke karkashin ikonsu kafin a yi zaman tattaunawar.

Dakarun Gwamnatin Yemen da ke fada da mayakan Huthi
Dakarun Gwamnatin Yemen da ke fada da mayakan Huthi AFP/AFP
Talla

Shugaban kasar Yemen Abdourabuh Mansour Hadi da yanzu haka ke samun mafaka a kasar Saudiya a ranar Juma’a da ta gabata ne ya sanar cewar za su shiga tattaunawa da ‘yan tawayen Huthi a zaman da aka shirya karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya a Oman

Amma a daren Lahadi shugaban ya sake fitar da sanarwar cewar ba bu batun zaman sulhu da mayakan sai idan ‘Yan tawayen sun amince da sanya hannun kan kudurin Mjalisar Dinkin Duniya na zaman lafiya tare da janyewa daga yankin Marib da ma sauran manyan garuruwan da yanzu haka ke karkashin ikon mayakan.

Ana dai cigaba da fafatawa tsakanin bangarorin biyu inda kuma Saudiya da kawayenta na Larabawa ke ci gaba da yi wa ‘Yan tawayen luguden wuta da jiragen sama.

Wannan dai ba shi ba ne karo na farko da bangarorin biyu ke kin amincewa da zaman sulhu domin kawo karshen rikicin kasar da ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da dubu hudu cikin su har da yara kanana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.