Isa ga babban shafi
Saudi Arabia

Makkah- Yarima Khaled al-Faisal ya mika sakamakon binciken su

Gwamnan makkah na kasar Saudiya Yarima Khaled al-Faisal ya mika rahotan sakamakon binciken musababbin aukuwar ruftawar karafan fadada ginin masallacin ka’abba wanda da ya yi ajalin mutane 107 zuwa ga hukumomin kasar. Sai dai kuma ba a bayyana ko me ke tatare da rahoton ba.

Gwamnan birnin Makkah Yarima  Khaled al-Faisal
Gwamnan birnin Makkah Yarima Khaled al-Faisal REUTERS/Saudi Press
Talla

A jiya Assabar ne dai Sarki Salman na saudiya ya sha alwashin bin didigin dalilin ruftawar karafan a dai-dai lokacin da dubun dubatan al’ummar musulmi mahajjata ke ibada a Masallacin.

Har yanzu dai ba a bayyana ko ‘yan wani kasa ba ne iftila’in ya ritsa da su a hukumance, sai da wasu rahotannin na cewa akwai ‘yan kasashen India da indonesia da Thailand cikin wadanda suka rasu.

Kana cikin mutane 238 da suka jikata akwai ‘yan kasashen Iran da Turkiya da Afghanistan da Masar da kuma Pakistan.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.