Isa ga babban shafi
Saudiya

Zamu gano dalilin rubtawar karafa a Ka'aba: Salman

Sarkin Saudiya, Salman ya lashi takobin gano musabbabin rubtawar karafan daukan kayayyakin gine-gine cikin Masallacin Ka’abah a ranar Jumma’a, tare da kashe mutane sama da 100.

Sarki Sal
Sarki Sal REUTERS/Gary Cameron
Talla

Sarkin ya bayyana haka ne bayan ya halarci inda hadarin ya faru kuma ya ce zasu sanar da jama’a sakamako da zaran an kammala bincike.

Tuni dai Sarkin na Saudiya ya aike da sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasu a hadarin tare da kuma ziyartar asibitin An-Noor domin duban lafiyar wadanda suka jikkata.

Duk da faruwan wannan al-amarin dai hakan bai zai hana gudanar da aikin Hajji ba kmar yadda aka saba duk shekara, inda dubban al-ummar Musulmi daga sassan duniya ke taruwa domin bautan Allah.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.