Isa ga babban shafi
Thailand

An sake bude wurin ibada da aka kai harin bom a Bangkok

Hukumomin Kasar Thailand sun sake bude wajen ibadar mabiya addinin Budha inda aka kai harin bom wanda ya kashe mutane 21 yayin da ‘Yan Sandan kasar suka kaddamar da farautar mutumin da ake zargi ya dasa bam din da ya jikkata masu ziyara a wajen ibadar.

'Yan sanda sun kaddamar da farautar wanda ya kai hari a wajen ibadar Erawan a Bangkok
'Yan sanda sun kaddamar da farautar wanda ya kai hari a wajen ibadar Erawan a Bangkok REUTERS/Kerek Wongsa
Talla

An kai harin ne a ranar Litinin a lokacin masu ibada da ‘yan yawon bude ido suka cika makil a wajen ibadar da ake kira Erawan a Bangkok.

Rahotanni sun ce cikin wadanda suka mutu har da ‘Yan kasashen waje 11 da suka fito daga China da Hong Kong da Singapore da Indonesia da Malaysia, yayin da wasu sama da 100 suka samu raunuka.

Babu dai wata kungiya da ta yi ikirarin kai harin. Amma masu bincike sun yi imanin da cewa wanda ya kai harin yana da wadanda suka taimaka ma shi.

Mahukuntan Thailand kuma sun yi alkalin kudin lada dala 28,000 ga duk wanda ya taimaka da bayani akan maharin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.