Isa ga babban shafi
China

Hukumomin China sun haramta wa musulmin kasar yin azumi

Yau Alhamis al’ummar Musulmin duniya suka fara azumin watan Ramadana, daya daga cikin shika shikan addinin Islama.Rahotanni daga sassan duniya adabam dabam suna nuna cewar yau alhamis ce daya ga watan Ramadana kamar yadda hukumomi da shugabanin addini suka sanar. 

Shugaban kasar China, Xi Jinping tare da wasu shugabannin Musulmi 'yan kabilar Urumqi
Shugaban kasar China, Xi Jinping tare da wasu shugabannin Musulmi 'yan kabilar Urumqi Reuters/路透社
Talla

Sai dai kuma hukumomin ksar Sin wato China, sun hana ma’aikatan gwamnati, daliban makarantu da malamai yin azumin na Ramadan, a yankin Xinjiang dake da akasarin Musulmi.
Sanarwar da hukumomin kasar suka sanya a shafin su na Internet, ta kuma bayar da umarnin bude dukkan shagunan sayar da abinci a yankin na Xinjiang, tare da hana yi sallolin dare da aka saba yi a watan na Ramadan.
Jam’iyyar Communist mai mulkin China bata bayan kowane addini, kuma ta shafe shekaru da dama tana haramta yin azumi a wannan yankin, mai akasarin ‘yan kabilar Uighur tsiraru mabiya addinin Islama.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.