China
Babu wanda ya tsira a hatsarin jirgin ruwan China
Jami’an gwamnatin kasar Sin sun ce zai yi wuya a sami wanda ya tsira da ransa a hatsarin jirgin ruwan da ya nutse da masu yawon bude ido sama da 400. An tabbatarwa ‘yan uwan wadanda ke cikin jirgin ruwan hakan ne, bayan da aka tsamo jirgin da ya nutse da kusan mutane 460, a ranar litinin da ta gabata.
Wallafawa ranar:
Talla
Zuwa yanzu mutane 14 ne kawai suka tsira daga hatsarin, kuma an sami gawarwakin wasu kusan 100 amma daruruwa ne suka bata.
Ana hasashen mutane 442 suka mutu ko suka salwanta, al’amarin da aka danganta mafi muni a tsawon shekaru 70 a China.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu