Isa ga babban shafi
Yemen-Saudiya

Saudiyya za ta tsaigata wuta a Yemen

kasar Saudiyya ta gabatar da shirin tsagaita bude wuta a yemen na kwanaki 5, domin bawa kungiyoyin agaji damar shiga cikin kasar don kai agaji akan fararra hula.Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry da ke ziyara a Saudi Arabia shima ya goye bayan shirin inda ya umarci ‘yan tawayen Yemen da ke samun goyon bayan Iran da su amince da tsagaita bude wutar.

halin da kasar Yemen ke ciki
halin da kasar Yemen ke ciki REUTERS/Khaled Abdullah
Talla

Minister Harkokin wajen kasar Saudiya Adel-al-Jubeir ya sanar da bukatar tsaigata bude wutar ne, bayan wata ganawa da sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry a birnin Riyadh, inda ya ke cewa hakan zai bada daman bada taimakon gagawa a yemen

Sai dai Jubeir bai sanar da ranar fara tsaigata bude wutar ba

Ana sa bagaran John Kerry ya ce za’a iya cimma bukatun kawai ne, idan an samu amincewar mayakan Huthi

Kerry yayi kira mai karfi ga ‘yan tawayen Huthi da su amince da wannan tsaigata bude wuta, domin bada daman taimakawa mabukata a Yemen da kuma cimma matsaya guda na zaman lafiya

Rahotannin dai na cewa Hare-hare bama-bamai da kasashen kawance karkashin jagoranci Saudiya ke kaiwa kasar Yemen, har yanzu bai tabuka komai ba akan rikicin kasar Yemen, lura da yadda mayakan Huthi ke cigaba da karfi, yakin da a kullum ke lakume rayukan alummar kasar musamman fararra hula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.