Isa ga babban shafi
China

China ce kasa ta uku wajen sayar da makamai a duniya-Rahoto

Kasar china ta zama kasa ta uku, bayan Amurka da Russia dake gaba gaba wajen sayar da makamai a duniya

Makamai a Afrika
Makamai a Afrika REUTERS/Sia Kambou/Pool
Talla

Rahotan da cibiyar zaman lafiya dake Stockholm ke fitarwa a kowace shekerar na cewa hakan ya biyo bayan habbaka da kasar china tayi a fanin sayar da makamai da maki 16 cikin 100 a cikin shekaru 5 da suka gabata.

Rahotan dai ya bayyana kasar amurka a matsayin kan gaba da maki 31 cikin dari dake sayar da manyan makamai a duniya, Sai Russia wacce itace ta biyu da maki 27 cikin dari, kafin china.

Kasar jamus ita ta kasance kasa ta hudu yayin da fransa ta zo ta biyar

Cibiyar ta kuma bayyana cewa kashi biyu cikin uku na makamai ana sayar da sune a yankuna Asia musamman kasar Pakistan wanda kashi 41 cikin dari na makamai acan aka fi cinikin su, sai kasar Bangladesh dake bi mata, kana Myanmar
yayin da kasar china ta fi sayar da makaman a yankuna afrika 18, yayyin da makaman Russia aka fi cinikin su a India.

A yankuna afrika, Algeria itace kan gaba wajen sayan makamai daga kasashen, sai morocco dake bi mata, sai kasar najeria da kamaru wanda ke sayan nasu makaman daga kasashen dabam-dabam domin gaggauta cima muradan su na yaki da yan ta’ada kamar yadda cibiyar ta rawaito
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.