Isa ga babban shafi
Isra'ila-Falesdinu

Isra'ila da Falasdinu zasu koma teburin sasantawa

Yau Lahadi ake sa rai bangariorin Kasar Isra’ila da na Palasdinawa dake rikici da juna zirin Gaza, zasu koma teburin sasantawa kai tsaye, tare masu shiga tsakani daga kasar Masar. Ana fatan tattaunawar zata taimaka wajen samar da zaman lafiya na din din din, kafin yarjejeniyar tsagaita wutar da ke aiki yanzu haka, ta kawo karshe.Dama hukumomin birnin Alkahira sun nemi dukkan bangarorin su amince a kawo karshen rikicin, da zuwa yanzu ya lakume rayukan Palasdinawa kusan 2000, da Yahudawa 67 mafi yawansu sojoji. 

Wani gini da rikicin Gaza ya rutsa da shi
Wani gini da rikicin Gaza ya rutsa da shi REUTERS/Finbarr O'Reilly
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.