Isa ga babban shafi
Indonesia

An rufe wuraren sheke Aya a kasar Indonesia domin Ramadana

A yayin da ake shirin shiga Watan Ramadana hukumomi a kasar Indonesia, sun baza daruruwan ‘yan sanda da soji, da suka kaddamar da aikin rufe wuraren da ake masha’a a gari na biyu mafi girma a kasar wato Surabaya

buddhistchannel.tv
Talla

Wannan aikin dai an soma shi ne, lura da yanda ake gaf da shiga Watan Ramadana Wata mai tsarki da daukacin Musulman Duniya ke mutuntawa daga cikin Kalandar Musulunci.

A ka’idar Addinin musulunci dai idan lokacin Azumin Ramadana ya shigo, Malaman Addinin musulunci a dukkanin fadin Duniya kan karkata hankalinsu ne ga Karantawa da fassara Ayoyin al-Qur’ani mai tsariki, abin da ke zaman tunatarwa ga al’ummar Musulmi dangane da koyarwar Addinin da bayyana umurnin Ubangiji ko hani.

Wani jamiin Gwamnati dake jagorantar aikin tarwatsa wuraren sheke Ayar, ya fadi cewa suna wannan aikin ne domin ganin an shiga watan azumi ba tare da wasu munanan ayyuka da mutane ke aikatawa ba.

Yanzu haka dai hankullan Musulmin Duniya sun karkata ne ga sauraron sanarwar ganin Watan da shugabannin al’ummar Musulmin kan yi bisa al’ada a kowace Shekara.

Watan Ramadana dai na daga cikin Watannin Musulunci da a dabi’ance Musulmin Duniya ke kulawa da ranakun somawa, ko kuma karewarsu.

Al’ummar Musulmi kan yi buki na musamman da ake kira Sallah, bayan kammala Azumin Ramadana a kowace shekara.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.