Isa ga babban shafi
Indonesia

Mutane 15 sun mutu bayan da dutsen ya yi aman wuta a Indonesia ya

Aikin ceton da ake ci gaba da yi bai bada damar samun wani abu mai rai ba, a yankunan dake gab da tsaunin nan mai aman wuta na kasar Indunisiya na Sinabung bayan da ya yi numfashin da ya haddasa hasarar rayukan mutane 15.Shugaban tawagar masu aikin ceto Laftana Kanar Asep Sukarma, ya bayyana cewa bai yi zaton samun wani dai rai ba a yankin bayan furjin wutar da wannan tsauni yayi.Wani mazaunin yankin yace ba kowa a kauyen Sukameriah da aman wuta ya afkawa, kuma akasarin gidaje sun rushe, wadanda kuma suka rage a tsaye, toka ta lullube su.Mai aiki ceto sun ce sautin kawai ta suka ji a wurin, shine wata wayar hannu da ke kara a cikin wata jikkar daba a san mai ita ba. 

masu aiki ceto sun dauko wani da hadarin aman wutar dutse ya rutsa da shi
masu aiki ceto sun dauko wani da hadarin aman wutar dutse ya rutsa da shi REUTERS/S Aditya
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.