Isa ga babban shafi
Indonesia

Aman Wuta A Kasar Indonesia

Tsaunin Sinabung dake kasar Indonesia yayi aman wuta yau littini karo na biyu inda bakin hayaki da toka suka  yamutsa sararin samaniya.Ala tilas aka soke sauka da tashin jiragen sama na wani lokaci a yankin, yayin da mutane sukayi ta tserewa domin neman mafaka.Bakin hayaki da toka nata tashi sama da bazuwa har kimanin mita 2,000 kamar yadda wani masanin Aman wuta daga tsaunuka Agus Budianto ke cewa.Wannan aman wutan na yau yafi na jiya.Mutane akalla 3,000 ne suka tsere domin neman mafaka yau.Kamar yadda wani Jamiin Hukumar Kare Haddura na Gwamnatin kasar, Andes Mbaga ke cewa yawan wadanda suke bukatar mafaka yanzu sun kai 21,000.Hukumomin kasar sun nemi jamaa dake tsakanin kilometre shida dake wajen dasu bar harabar.  

Aman wuta yau a tsaunin Sinaburg na kasar Indonesia
Aman wuta yau a tsaunin Sinaburg na kasar Indonesia rfi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.