Dutsi mai amon wuta ya yi ta’adi a Indonesia
Mutane biyu ne aka ruwaito sun mutu a ƙasar Indonesia bayan da Dutsi mai amon wuta ya turmuƙe da hayaƙi tare da yin watsi da duwatsu da suka abkwa gidajen mutane a yankin Java. Rahotanni sun ce wasu mutane ne ƴan shekaru 60 guda biyu suka mutu a yankin Malang da ke lardin tsibirin Java.
Wallafawa ranar:
Dubban Mutane ne suka kauracewa gidajensu bayan dutsin na Kelud ya fara fitar da amon wuta.
Wannan ne kuma ya sa aka rufe Tasoshin jiragen sama a Shuraya da Solo da Yogyakarta saboda rashin ganin haske a dogon zango.
Tun lokacin da Dutsin zai fara fitar da amon wuta ne mahukuntan ƙasar suka bukaci ɗaruruwan mutanen da ke zama kusa da tsaunin su ƙaurace.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu