Isa ga babban shafi
Isra'ila

Isra’ila ta tsaurara tsaro a yankunan Falesdinawa

Kasar Isra’ila ta kara tsaurara matakan tsaro a Yamma da Kogin Jordan, tare da sake cafke Falesdinawa 65 a yunkurin da kasar ke yi na ganin an sako wasu yara guda uku aka sace da Isra’ila ke zargin Hamas.

Mahmud Abbas na Falesdinawa da  Benjamin Netanyahu Firaministan Isra'ila
Mahmud Abbas na Falesdinawa da Benjamin Netanyahu Firaministan Isra'ila REUTERS/Mohamad Torokman/Sebastian Scheiner/Pool
Talla

Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas ya yi kakkausan suka akan matakan da Isra’ila ta dauka tare yin Allah waddai da wadanda suka sace Yaran yahudawa.

Mutanen Kasar Isra’ila sun kaddamar da yekuwa ta musamman a shafukan sadarwa na Intanet mai dauke da taken #Bringbackourboys# kamar yadda aka kaddamar da irin wannan yekuwar a Najeriya bayan sace ‘Yan mata sama da 200 a garin Chibok.

Mutanen Isra’ila sun nemi a sako Yaran a shafukan Facebook da Twitter, wadanda aka sace tsawon mako guda.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya zargi mayakan kungiyar Hamas da cewa su suka sace matasan, tare da umartar a tsaurara dukkan bincike a yankin Gaza domin gano inda aka boye su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.