Isa ga babban shafi
India

Modi zai datse yawan Ministocin India

Rahotanni daga India sun ce Sabon Firimiyan kasar Narendra Modi zai datse yawan Ministocin kasar tare da ayyana kansa a matsayin Ministan tsaro. Jaridun kasar sun ce bayan kammala bikin rantsar da Firimiyan ne zai bayyana matakin.

Narendra Modi sabon Firimiyan kasar India
Narendra Modi sabon Firimiyan kasar India REUTERS/Amit Dave
Talla

A yau Talata ne za’a rantsar da Narendra Modi wanda Jam’iyyarsa ta BJP ta samu rinjaye a karon farko tsawon shekaru 30 a India.

Kamfanin dillacin Labaran kasar India da wata kafar Telebijin sun ruwaito cewa Modi zai datse yawan Ministocin gwamnati zuwa 41, sabanin 71 a gwamnatin Firaminista mai barin gado Manmohan Singh.

Haka kuma wasu Jaridun kasar sun ruwaito cewa Modi zai nada kansa a matsayin Ministan tsaro yayin da kuma zai zabi shugabar Mata a Jam’iyyarsa Sushma Swaraj a matsayin Ministar harakokin waje.

Wannan mataki dai zai sa a rage yawan ma’aikatu a cikin kasar India.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.