Isa ga babban shafi
India

Indiya ta amince da maza-mata a matsayin jinsi na uku na al'umma

Kotun kolin kasar Indiya ta amince da maza-mata a matsayin jinsi na uku na al’umma da ke da dukkanin hakkokin da ya kamata a bai wa mata ko kuma maza a kasar.  

aurar da kananan yara a India
aurar da kananan yara a India Wikimedia Commons/Adarshsamaj
Talla

Hukuncin kotun ya bukaci gwamnatocin jihohi da kuma na tarayyar da ssu dauki maza-mata a matsayin jinsi na uku na al’umma a hukumance, kuma a ba su dukkanin hakkokin da suka wajaba.

Wannan dai na nufin cewa akwai jinsi na uku na dan adam a kasar ta Indiya, kuma kamar yadda mai shari’a Radha-krishnan alkali a kotun kolin ya bayyana, ba wai an yanke hukuncin ne saboda dalilai na jinkai ko kuma na kiwon lafiya ba, sai dai saboda batutuwa na kare hakkin bil’adama.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.