Isa ga babban shafi
Thailand

Shugabannin masu zanga-zanga a kasar Tahiland sun bukaci haduwa da Firaiminista

Wani lokaci a yau ne aka zaci cewar shugabannin masu zanga-zanga a kasar Thailand ke shirin haduwa da Firaiministar kasar Tahiland Yigluck Shinawatra domin tattaunawa kan jerin bukatun su.

Masu zanga-zanga a Thailand
Masu zanga-zanga a Thailand REUTERS/Dylan Martinez
Talla

Sai dai labarin da ke fitowa daga kasar ta Thailand yazu haka na nuna cewar Firaiministar ta ki amincewa da bukatar shugabannin masu zanga-zangar ta kyamar gwamnati.

Masu zanga-zangar dai na neman kifar da gwamnatin Firaiministar ne, da kuma maye gurbinta da Majalisar mutanen kasar.

Firaiministar ta bayyana cewar zatayi komai take ta tabbatar ta dadadawa al’ummarta, amma a matsayinta na Firaiminista, duk abinda za ta yi dole ya kasace a karkashin tanadin kundin tsarin mulkin kasar.

Wannan dai shi ne karon farko da Firaiministar ta yi magana da kafaifan watsa labarai akan wannan batu, tun bayan barkewar tashin hankali a kasar.

A ranar lahadi ma, jami’an gwamnatin kasar sun ce tashin hankalin siyasar da ke faruwa a kasar ta Thailand ya yi sanadiyyar mutuwar a kalla mutane Biyu 2, yayin da wasu 42 suka sami munanan raunuka.

Masu adawa da magoya bayan gwamnatin dai sun baiwa hammata Iska a Daren Assabar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwa da raunata mutanen da dama.

Haka ma ‘yan sanda sun harba Hayaki mai sa Hawaye, kan masu zanga zangar da suka afka gidan a gwamnati, da nufin kifar da gwamnati Firaiminista Yingluck Shinawatra, bayan sun shafe kwanaki a kan titunan kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.