Isa ga babban shafi
Isra'ila

Isra'ila ta nemi a gaggauta gine-gine a gabashin Jerusalem

A yau Laraba, hukumomin kasar Isra’ila sun nemi a ci gaba da gina gidajen ‘yan share waje zauna, a yankin gabashin Jerusalam. Wannan na zuwa ne kwana guda, bayan kasashen dunmiya sun yi Allah wadai da shirin gine ginen.Ministan leken asirin kasar ta Yahudu Yuval Steinitz, da ya nemi a ci gaba da gine ginen, yace Benjamin Netanyahu ya yi daidai, da ya ce a lokacin irin wannan, da ake zaman dar dar, da kuma hukumomin kasar ta Yahudu ke kokarin samun goyon bayan kasashen yammacin duniya, dole ayi aikin ba kakkautawa kuma cikin dabara.Jiya Talata da maraice, Netanyahu ya bayar da sanarwar soke shirin gina wasu gidaje dubu 20 a yankin na gabashin Jerusalem, sa’oi kadan bayan sanarwar gina su ta sami shan suka, daga kasashen Amurka da Palasdinu.Sai dai mai Magana da yawun Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, wato Jennifer Psaki ta ce, bai kamata gina gidajen ya zaman dalilin dakatar da sasanta bangarorin 2 ba.Psaki na mai cewa kara da cewa cimma matsaya da kuma kulla yarjejeniya, shi ne muhimmin abu ga dukkanin bangarorin biyu wato Isra’ila da Palasdinawa. Ta ce bai kamata batun gina matsugunan Yahudawa a yankunan da Israel ta mamaye ya kasance hujjar da za a yi amfani da ita domin wargaza tattaunawar da ake yi ba. Saboda haka ya kamata a ci gaba da tattaunawa domin warware wannan takaddama.A wata sabuwa kuma, yau laraba wani matashi Palasdine, ya kashe sojan Isra’ila daya, ta hanyar soka mishi wuka, a cikin wata motar bus, a arewacin kasar ta Yahudu. 

Praiministan Isra'ila Benyamin Netanyahu.
Praiministan Isra'ila Benyamin Netanyahu. REUTERS/David Buimovitch/Pool
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.