Kotun China ta yi watsi da daukaka karar Xilai
Wata Kotun daukaka kara a kasar China, taki amincewa da daukaka karar da fitaccen Dan siyasar kasar Bo Xilai ya yi kan hukuncin daurin rai da rai da aka masa, bayan samunsa da laifin cin hanci da almubazzaranci da kuma amfani da ofishinsa ta hanyar da bata kamata ba.
Wallafawa ranar:
Wannan hukunci da kotun Shandong ta yanke, ya kawo karshen duk wata fafutuka na sauya hukuncin da Bo Xilai ke bukata, na ganin ya wanke kansa daga tuhume tuhumen da aka masa na cin hanci da rashawa.
Kafin shekarar 2012, Bo Xilai na daga cikin manyan ‘Yan siyasar China kuma shugaban birnin Chongqing, da ke kudu maso Yammacin kasar.
Wannan hukunci, ya kawo karshen siyasar Bo Xilai, kamar yadda lauyansa ya bayyana, kuma yana da wuya a sake ganin sa a bainar jama’a.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu