Isa ga babban shafi
China

An kawo karshen shari’ar Xilai, ana jiran hukunci

A kasar China an kawo karshen shari’ar da ake wa attajirin kasar, Bo Xilai, Amma Masu gabatar da kara sun nemi a yanke masa hukunci mai tsauri akan tuhumar da ake masa na laifin kisa da cin hanci da Rashawa.

Bo Xilai yana jawabi, a lokacin da ya gurfana a gaban kotun kasar Sin
Bo Xilai yana jawabi, a lokacin da ya gurfana a gaban kotun kasar Sin
Talla

Tuhume tuhumen da ake wa Xilai ya kasance babban batu a kasar China.

Anan gaba ne ake jiran kotun ta bayyana hukuncin da aka yanke wa Xilai wanda aka kama da laifin bayar da toshiyar baki da yin fatali da kudi wanda baraka ne ga babbar jam’iyyar kwaminisanci da ke mulki a kasar.

Masana suna ganin tuni, an yanke shawarar hukunci mai tsauri da za’a yanke wa Xilai, wanda jigo ne a jam’iyya mai mulki a China.

Karkashin dokar China, hukuncin kisa ake yanke wa wanda aka kama da laifin cin hanci da rashawa da suka haura kudin kasar yuan 100,000.

Amma tun fara zaman shari’ar ta kwanaki biyar Bo Xilai ke musanta zargin da ake masa.
Akwai matar Xilai da ake zargi ta kashe wani attajirain Birtaniya, inda a lokacin mijinta ya nemi mafaka a ofishin jekadancin Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.