Bo Xilai, ya sake bayyana a gaban kotun kasar Sin
Masu shiggar da kara a kasar Sin na zargin Bo Xilai da karbar sama da kudin dalar Amurka dubu 163 daga hanun wani attajiri da ake kira Tang Xiaolin.
Wallafawa ranar:
Fitaccen dan siyasar kasar China, Bo Xilai, wanda ya sake bayyana a gabban kotun kasar , ya ki amsa tuhumar da ake masa ta karbar cin hanci da rashawa.
Tuhumar da akewa Xilai bisa karbar cin hancin da rashawa ita ce ta farko cikin laifukan da ake zargin shi da aikatawa da ya sabawa dokokin kasar ta Sin.
Xilai dan shekaru 64 da haifuwa na sa ran gaskiya ta bayyana duk da zargin da ake masa da shi da iyalen sa na karbar kudade tareda aikata kisa kan wani dan kasar Birtaniya mai suna Neil Heywood a watan Agusta na shekara ta 2012.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu