Bo Xilai ya fara rayuwa a gidan yari
Tsohon Babban jami’in Jam’iyyar Kwaminisanci, Bo Xilai, ya fara zama a gidan yari, sakamakon daurin rai da rai da wata kotu ta yi masa, bayan ta same shi da laifin cin hanci da rashawa. Kotun tace ta samu Bo da anfani da mukaminsa ta hanyar da bata kamata ba, saboda haka ta sanar da haramta masa harkokin siyasa har abada, da kuma kwace daukacin kadarorinsa.
Wallafawa ranar:
A bara ne aka tube Mista Bo daga mukaminsa saboda badakalar cin hanci da kuma matarsa da aka kama da laifin ta kashe attajirin Birtaniya Neil Heywood.
Kotun ta yanke hukuncin ne bayan an kama Bo da laifin ya karbi cin hanci na kudi da suka kai Yuan miliyan 20.4 na kudin China. Kuma Kotu ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 15 akan almubazzaranci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu