Isra’ila ba ta da hurumin yin adawa da daga darajar Falasdinawa- Olmert
Tsohon Firaministan Isra’ila, Ehud Olmert, yace ba su da hurumin kin amincewa da daga darajar kasar Falasdinu a matsayin ‘Yar kallo a zauren Majalisar Dinkin Duniya. Ya kuma ce gina sabbin gidaje a yankunan Falasdinawa bai dace ba.
Wallafawa ranar:
Olmert wanda ake saran zai bayyana shirinsa na shiga takarar zabe mai zuwa, yace shirin Isra’ila na gina sabbin gidaje a Yankunan Falasdinawa bai dace ba, yana mai cewa lokaci na kurewa na tattaunawa da Falasdinawa domin samun dawamammen zaman lafiya.
A ranar 29 ga watan Nuwamba ne Falasdinawa suka samu nasarar samun kujerar 'Yan kallo a zauren Majalisar Dinkin duniya bayan kwashe shekaru suna gwagwarmaya duk da adawar Isra'ila da Amurka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu