Isa ga babban shafi
Sri Lanka

Kotun soji ta samu Janar Fonseka da laifi

WATA Kotun soji a kasar Sri Lanka, ta samu Tsohon Babban Hafsan sojin kasar, Janar Sareth Fonseka, da laifin shiga siyasa, inda ta tube masa mukaminsa na Janar da kuma kwace duk kyaututukan da ya samu.Wata majiya a Colombo, ta shaidawa kanfanin Dillancin labaran Faransa cewar, dazu ne aka karantawa Janar din hukuncin, kuma ana fatar shugaban kasar zai amince da shi.An dai fara shari’ar ne watanni biyar da suka gabata, kuma an bayyana cewar, Janar Fonseka nada damar daukaka kara.An dai samu baraka tsakanin shugaban kasa, Mahinda Rajakpase da Janar Fonseka, bayan kamala yaki da kungiyar Yan Tawayen Tamil Tigers, inda kowa ke ikrarin jagorancin nasarar, abinda ya sa Fonseka ya aje mikaminsa, inda ya shiga takarar zabe.Bayan samun nasarar zabe, shugaba Rajakpase ya tsare Janar Fonseka, inda ya zarge shi da shiga siyasa yayin da yake sanye da rigar aiki, da kuma cin hanci da rashawa.Kama jami’in ya janyo suka daga kasashen duniya, amma hakan bai hana gurfanar da shi a gaban kotun soji ba.Yanzu haka, Fonseka na fuskantar shari’ar cin hanci a wata kotu ta dabam. 

Janar Sarath Fonseka
Janar Sarath Fonseka AFP/Lakruwan Wanniarachchi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.