Isa ga babban shafi

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane dubu 800 na cikin hatsari a Sudan

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa akalla mutane dubu 800 dake Sudan na rayuwa a cikin hadari, saboda tsanantar rikice rikice da ka iya zama sanadiyar barkewar kazamin rikicin kabilanci a sassan Kasar. 

Wasu da rikicin Sudan ya daidaita
Wasu da rikicin Sudan ya daidaita REUTERS - ZOHRA BENSEMRA
Talla

An dai shafe tsawon Shekara daya da yaki ya barke tsakanin dakarun kasar da rundunar kai daukin gaggauwa ta RSF, wanda ya yi sanadiyar haifar da adadi mafi yawa na mutanen da rikici ya daidaita a duniya.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane kusan miliyan 25, wato rabin yawan alummar Sudan ke bukatar taimakon agaji, yayin da ta ce wasu mutanen miliyan 8 ne suka tsere daga gidajen su. 

Jagorar harkokin siyasa na Majalisar, Rosemary DiCarlo ta Shaidawa mambobin Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewa sannu a hankali rikicin da ke tsakanin dakarun RSF da sojijin Sudan na dab da shiga El Fasher dake yankin arewacin birnin Darfur

DiCarlo ta ce sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi gargadin cewa fada a El Fasher ka iya zama sanadiyar barkewar kazamin rikicin kabilanci a sassan birnin Darfur. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.