Isa ga babban shafi

Mauritania ta bukaci taron G7 ya janye takunkuman kasashen yamma kan Afrika

Yau Juma’a ake shirin ƙarƙare taron ministocin wajen ƙasashen ƙungiyar G7 da ke gudana a Italiya, taron da ya mayar da hankali kan rikicin gabas ta tsakiya da kuma yaƙin Ukraine da Rasha, sai kuma wasu matsaloli da suka dabaibaye nahiyar Afrika.

Shugaba Mohamed Ould Ghazouani na Mauritania.
Shugaba Mohamed Ould Ghazouani na Mauritania. © Amanuel Sileshi / AFP
Talla

Ministan harkokin wajen Mauritania Mohamed Salem Ould Merzoug da ya jagoranci sashe na musamman yayin taron na G7 ya bukaci shiga tsakanin ƙungiyar wajen warware wasu matsaloli da nahiyar ta Afrika ke fama da su ciki har da janye takunkumai kan wasu kasashe.

Ould Merzoug ya bukaci hadin gwiwar G7 da ƙungiyar AU don warware matsalolin da ƙaƙaba takunkuman kasashen yammaci ya haddasawa ƙasashe da dama a nahiyar ta Afrika, musamman Zimbabwe.

Kiran na Ould Merzoug na zuwa ne a dai dai lokacin da ake tsaka da tattaunawa tsakanin Italiya da Amurka a kokarin kulla wasu yarjeniyoyi tsakaninsu da Afrika.

Yayin taron na tsibirin Capri da aka faro a Larabar makon nan ake kuma shirin ƙarƙarewa a yau Juma’a ya haddasa rabuwar kai tsakanin kungiyar ta G7 da AU musamman bayan amince da sabbin takunkumai kan Iran batun da kungiyar ta Afrika ba ta goyon baya.

Tawagar ministocin wajen na G7 sun amince da ladabtar da Iran ta hanyar ƙaƙaba mata sabbin takunkumai game da harin ramuwar gayyar da ta kai Isra’ila, batun da ya yi hannun riga da manufofin ƙungiyar AU.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.