Isa ga babban shafi

'Yan fashin tekun Somalia sun sako jirgin Bangladesh bayan karbar kudin fansa

‘Yan fashin tekun Somalia sun sako wani jirgin ruwan dakon kaya mai tutar Bangladesh tare da ma’aikatansa 23 a yau lahadi, bayan da masu jirgin suka biya kudin fansa, in ji kamfanin.

Dakarun India saman jirgin ruwan da 'yan fashin suka kama
Dakarun India saman jirgin ruwan da 'yan fashin suka kama © Indian Navy via AP
Talla

Jirgin ruwan MV Abdullah wanda ke jigilar kusan tan 55,000 na kwal daga Mozambique zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa, wasu gungun 'yan fashin teku da dama ne suka shiga da shi a nisan kilomita 1,000 daga gabar tekun Somalia wata guda da ya gabata.

Jirgin dakon kaya na MV Ruen
Jirgin dakon kaya na MV Ruen © indiannavy

"Mun cimma yarjejeniya da 'yan fashin," in ji Mizanul Islam, na kamfanin SR Shipping, mallakin kungiyar KSRM ta Bangladesh.

A cikin watan Maris, dakarun sa kai India sun kutsa cikin jirgin ruwan Malta MV Ruen, wanda 'yan fashin tekun Somalia ke rike da shi tun watan Disambar 2023. Wannan dai shi ne nasara na farko da aka samu na fashin teku a gabar tekun Somalia tun shekara ta 2017.

Yakin Somaliland
Yakin Somaliland © Studio FMM

Ma'aikatan jirgin su 17, 'yan Bama 9, 'yan Bulgaria bakwai da kuma dan Angola guda, an ceto su ba tare da wani rauni ba, sannan an kai 'yan fashin 35 zuwa Bombay na kasar India domin gurfanar da su a gaban kuliya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.