Isa ga babban shafi

Mahamudu Bawumia dan takara a Ghana ya bayyana matsaya mai tsauri kan masu auren jinsi

Dan takarar jam'iyya mai mulki a kasar Ghana Mahamudu Bawumia ya dauki bayana adawa tare da sanar da matsayin sa na mai kalubalantar masu ra’ayin auren jinsi a kasar.

Majalisar dokokin kasar Ghana yayin zaman tattauna dokar hana auren jinsi
Majalisar dokokin kasar Ghana yayin zaman tattauna dokar hana auren jinsi © Misper Apawu / AP
Talla

Mataimakin shugaban kasar Ghana Mahamudu Bawumia, kuma dan takarar shugaban kasa na jam'iyya mai mulki, a yau Alhamis ya bayyana matsaya mai tsauri a kan masu ra’ayin auren jinsi, yana mai jaddada adawarsa ga abinda ya kira cewa ya sabawa ka'idojin addini.

A cewar dan takarar,’yan siyasa na kokarin amfani da wannan al’amari a faggen siyasa da nufin canza tunanin jama’a a wannan kasa da ake kalo a matsayin kasar da ke mutunta addini da girmama al’adu na iyaye da kakkani.

Muhamadu Bawumia dan takara a jam'iyya mai mulkin kasar Ghana
Muhamadu Bawumia dan takara a jam'iyya mai mulkin kasar Ghana © Nipah Dennis / AFP

Wannan al’amari na ta’azara ne tun bayan da majalisar dokokin kasar ta zartar da dokar da ta haramta auren jinsi,wanda hakan ya kai wasu daga cikin kungiyoyi neman ganin an ba su damar cin karnen sub a babbaka,dan siyasar ya ce hakan ba zai yiyu ba.

Yayin da ake shirin gudanar da zabe a watan Disamba a kasar ta Ghana domin zaben wanda zai gaje shugaba Nana Akufo-Addo, batun 'yancin masu ra’ayin auren jinsi na kara raba kawunan yan siyasa,wanda hakan ya fito fili.

Da yake jawabi ga dubban musulmi a birnin Kumasi, birni na biyu mafi girma a Ghana a yau Alhamis a lokacin da ake gudanar da addu’o’in bukukuwan Sallah, dan takarar Mahamudu Bawumia ya yi sharhinsa na farko a bainar jama’a kan wannan batu mai cike da takaddama.

Mahamudu Baduwumia, dan takara a jam'iyyar NPP na kasar Ghana
Mahamudu Baduwumia, dan takara a jam'iyyar NPP na kasar Ghana © Luc Gnago / REUTERS

Mahamudu Bawumia ya na mai cewa "a kan batun auren jinsi yana da kyau a lura cewa al'adu da dabi'unmu na al'umma sun sabawa hakan."

"Bugu da ƙari, a matsayina na musulmi, ra'ayina game da wannan al'amari ya yi daidai da matsayin addinina. Don haka imanina ya yi tsauri sosai kan auren jinsi, kalaman dan takara a  jam'iyyar New Patriotic Party (NPP) mai mulki a zaben shugaban kasa da za a yi a watan Disamba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.