Isa ga babban shafi

Ana takaddama a Ghana saboda auren wani malamin gargajiya da matashiya

Takaddama ta barke a kasar Ghana bayan da wani malamin addinin gargajiya dan shekaru 63 ya auri wata matashiya mai shekaru 13, inda mutane da dama ke kira ga mahukunta da su kama shi.

Lalle na cikin al'adun Malam Bahaushe a lokacin bikin aure.
Lalle na cikin al'adun Malam Bahaushe a lokacin bikin aure. AP - Carley Petesch
Talla

Malamin addinin gargajiyar mai suna Nuumo Borketey Laweh wanda aka fi sani da Gborbu Wulomo ya auri yarinyar ne a gagarumin bikin da aka gudanar a wani karamin kauye dake wajen birnin Accra.

Tuni dai ‘yan sanda suka buda bincike kan wannan aure, yayin da jami’an tsaro suka killace yarinyar da mahaifiyarta don basu kariya, a cewa Ofishin Antoni Janar na kasar.

Bayanai na cewa idan har zargin da ake yi ya tabbata kan tsohon, zai fuskanci tuhumar cin zarafin kananan yara wanda hakan kuma ya ci karo da dokokin kasar, da ya kayyade shekaru 18 a matsayin shekarun aure.

Sai dai da yake kare kansa ta bakin mai magana da yawun sa, malamin addinin gargajiyar ya ce ba wai an kulla auren da yarinyar ne don ta sauke nauyin aurenta a yanzu ba, a’a za’a bata dama har sai ta kai shekaru 18 tukunna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.