Isa ga babban shafi

Mutane kusan miliyan uku da rabi na bukatar ceton gaggawa a Chadi - ACF

Kungiyar bayar da agaji da ke fafutukar kawar da matsalar yunwa ‘Action Against Hunger’, ta ce mutane fiye da miliyan 3 da dubu 400 ne ke bukatar agajin gaggawa a Chadi.

Wasu daga cikin dubban 'yan gudun hijirar da yakin Sudan ya raba da muhallansu.
Wasu daga cikin dubban 'yan gudun hijirar da yakin Sudan ya raba da muhallansu. REUTERS - ZOHRA BENSEMRA
Talla

Cikin sanarwar da ta rabawa manema labarai, kungiyar ta ACF ta ce bayyana kwararar dubban ‘yan gudun hijirar da ke tserewa yakin Sudan, da kuma karancin kudadden tallafin da take samu da ga hukumomin kasa da kasa, a matsayin dalilan da suka haddasa fuskantar gagarumin kalubalen a Chadi.

Kafin barkewar yakin Sudan a tsakiyar watan Afrilu na shekarar 2023, kididdigar Majalisar Dinkin Duniya ta nuna cewar Chadi na bai wa ‘yan gudun hijira sama da dubu 400 mafaka, wadanda rikicin yankin Darfur ya raba da muhallansu daga shekarar 2003 zuwa 2020. Sai dai sabbin alkaluma sun nuna cewar bayan barkewar yakin Sudan, adadin ‘yan gudun hijirar ya kai kusan dubu 900, kashi 88 cikin 100 kuma mata ne da kananan yara.

Baya ga dubban mutanen da take bai wa mafaka, kasar Chadi na da ‘yan gudun hijirar cikin gida da tashe-tashen hankula suka raba da muhallansu kimanin miliyan 1 da dubu 400.

A haliin yanzu kungiyar agaji ta ‘Action Against Hunger’ ta yi gargadin cewa yunwa za ta karu tsakanin kananan yara akalla dubu 480 tsakanin watan Oktoban shekarar bara zuwa Satumban bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.