Isa ga babban shafi

Hukumar WFP ta koka kan karancin kudaden tallafi a Kamaru

Hukumar samar da abinci ta majalisar dinkin duniya WFP, ta yi gargadin cewa rumbunan ajiyarta da kuma kudaden gudanarwa na gaf da karewa a Kamaru, lamarin da muddin ya tabbata, zai gurgunta ayyukanta na raba tallafin abinci ga dubun dubatar ‘yan gudun hijira a kasar.

Jami'an hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya a sansanin Minawao da ke kasar Kamaru.
Jami'an hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya a sansanin Minawao da ke kasar Kamaru. © ©UNHCR/Moise Peladai
Talla

Kididdigar Majalisar Dinkin Duniya ta nuna cewar ‘yan gudun hijira dubu  460,000 ke samun mafaka a Kamaru, fiye da dubu 220,000 daga cikinsu kuma sun fito ne daga kasashen Najeriya da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Mataimakin shugaban hukumar WFP a Kamarun Aboubacar Guindo, ya shaidawa gidan rediyon RFI cewar suna cikin fargaba kan tagayyarar da dubban mutane ka iya yi a sansanonin ‘yan gudun hijirar da ke karkashin kulawarsu, idan suka gaza samun daukin gaggawar da suke bukata.

Rikicin Boko Haram da aka kwashe shekaru ana fama da shi arewa maso gabashin Najeriya da kuma tashin hankalin da ake yi tsakanin kungiyoyi masu rike da muggan makamai a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, sun tilasta wa Kamaru karbar dubban 'yan gudun hijirar da suka tsere daga muhallansu, duk da cewar ita kanta Kamarun na fama da nata matsalolin tsaron da suka tilasta wa dubban 'yan kasar zama 'yan gudun hijirar cikin gida, baya ga wadanda suka fice daga kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.