Isa ga babban shafi
Kamaru-Chadi

Rikicin kabilanci ya sake kora mutane fiye da dubu 80 Chadi daga Kamaru

Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da mutane dubu 80 suka tsallaka Chadi daga Kamaru cikin kwanaki 10 da suka gabata, sakamakon tsanantar rikicin kabilanci a yankin Arewacin Kasar.

Wasu 'yan gudun hjirar Kamaru da ke samun mafaka a Chadi.
Wasu 'yan gudun hjirar Kamaru da ke samun mafaka a Chadi. REUTERS - Mahamat Ramadane
Talla

Hukumar kula da kaurar baki ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce abin damuwa ne matuka yadda ake samun karuwar wadanda rikicin ke tilastawa tsallakawa Chadin daga Kamaru tun bayan farowar rikicin a ranar 5 ga watan Disamba da ya kai ga rasa rayukan mutum 22 tare da jikkata wasu 30.

Babban jami’in hukumar da ke Chadi Papa Kysma Sylla ya ce zuwa yanzu ‘yan gudun hijirar Kamaru dubu 82 ne ke samun mafaka a Chadi yayinda a kowacce rana ake samun karuwar masu tsallakawa saboda tsanantar rikicin kabilancin.

A cewar jami’in karuwar ‘yan Kamarun da ke tsallakawa Chadi na zamowa babban kalubale a kasar mai yawan jama’a miliyan 17 wadda kuma ke bayar da mafaka ga dubunnan ‘yan gudun hijira baya ga ‘yan kasar da rikici y araba da muhallansu.

Shugaban mulkin Soji na Chadin Mahamat Idriss Deby Itno ya bayyana karuwar masu neman mafakar a matsayin babban kalubale garesu, yayinda ya bukaci hukumomi da manyan kasashe su shiga tsakani don bayar da agajin gaggawa.

Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce bayan rikicin tsakanin Masunta da Makiyaya da ya juye zuwa na kabilanci fiye da kauyuka 10 a arewacin kamaru ne suka koma toka, yayinda rikicin ke ci gaba da tsananta.

Alkaluma sun nuna cewa ko a makamancin rikicin na Masunta da Makiyaya cikin watan Agusta mutane 45 suka rasa rayukansu duk dai a yankin na Arewa mai nisan kasar Kamaru.

Kafin rikicin na baya-bayan nan dai, fiye da ‘yan gudun hijrar Kamaru fiye dubu 20 ke samun mafaka a Chadi ciki har da dubu 8 da 500 wadanda suka ki komawa gida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.