Isa ga babban shafi
Kamaru

Kamaru ta musanta rahoton korar 'yan gudun hijirar Najeriya

Gwamnatin Kamaru ta musanta rahotannin dake cewa, tana tilastawa ‘yan gudun hijirar Najeriya da suka tserewa rikicin Boko Haram komawa gida.

Wasu 'yan gudun hijirar Najeriya da suke tserewa rikicin Boko Haram a sansanin 'yan gudun hijira na Minawao dake arewacin kasar Kamaru. (18/02/2015).
Wasu 'yan gudun hijirar Najeriya da suke tserewa rikicin Boko Haram a sansanin 'yan gudun hijira na Minawao dake arewacin kasar Kamaru. (18/02/2015). REUTERS/Bate Felix Tabi Tabe
Talla

Kamaru ta mayarda da martani ne kan rahoton baya bayan nan da majalisar dinkin duniya ta wallafa, dake cewa gwamnatin kasar na korar ‘yan Najeriya da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu zuwa gida, duk cewa tana da masaniyar har yanzu, yankunan da ‘yan gudun hijirar suka tserewa na fuskantar barzanar hare-hare.

Cikin sanawar da ta fitar, gwamnatin Kamaru ta ce dukkanin ‘yan gudun hijirar da suka koma gida, sun yi hakan ne bisa ra’ayin kansu, amma ba tilas ba.

Tun bayan kazantar rikicin Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya, daga shekarar 2011 zuwa yanzu, wata kididdiga ta nuna cewa, sama da ‘yan kasar dubu 100, sun tsere zuwa cikin Kamaru domin samun mafaka a arewacin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.