Isa ga babban shafi

Habasha za ta kwashe jama'arta dubu 70 da ke fuskantar cin zarafi a Saudiya

Habasha za ta fara aikin kwashe ƴan kasarta akalla dubu 70 da ke zaune a Saudi Arabia ciki har da wadanda suka shiga ƙasar ba bisa ƙa'ida ba kuma su ke fuskantar cin zarafi ko takura a wuraren da suke aikin kwadago, shirin da Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar ke cewa za a fara cikin watan nan.

Dubun-dubatar 'yan Habasha ne rikici ko talauci ya tilastawa barin kasar don cirani a ketare.
Dubun-dubatar 'yan Habasha ne rikici ko talauci ya tilastawa barin kasar don cirani a ketare. AFP
Talla

Ministar Harkokin Wajen Habasha Birtukan Ayano da ke sanar da shirin fara aikin kwashe jama’ar kasar ta ce wannan ne karo na 3 da gwamnatin ke aiwatar makamancin shirin.

Shirin wanda Habasha ta faro tun a shekarar 2018 na da nufin kwashe ƴan kasar da suka tafi Saudi Arabia aiki amma kuma suka fada wahala ko ƙangin bauta.

Sai dai Ma’aikatar Wajen ta Habasha ba ta fayyace ko ƴan kasar da za a kwaso daga Saudiyan sun kunshi wadanda ke zaune da takardu ko kuma wadanda ke zaune ba bisa ƙa’ida ba.

Cikin sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta ce ofisoshin yanki ne za su tabbatar da isar kowa ga ahalinsa bayan kwaso su daga Saudi Arabiyan zuwa Addis Abba.

Ƙarkashin shirin gwamnatin Habasha za ta rika bai wa ƴan kasar da aka dawo da su kudade don gudanar da rayuwarsu.

Zuwa yanzu Habasha ta kwaso jama’arta akalla dubu 917 daga kasashen Saudiyya da makwabtanta ciki har da Yemen ƙarkashin shirin da aka ƙaddamar a 2018.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.