Isa ga babban shafi

Amnesty ta roki Macron ya hana Yariman Saudiya kashe wasu tarin matasa

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta roki shugaban Faransa Emmanuel Macron da ya matsa wa yarima mai jiran gadon sarautar Saudiya lamba kan ya saki wasu matasa bakwai da ke fuskantar hukuncin kisa a bisa laifukan da suka aikata yayin da suke kanana. 

Shugaba Emmanuel Macron yayin karbar bakoncin Yarima mai jiran gado na Saudiya Mohammed bin Salman a fadar Elysée.
Shugaba Emmanuel Macron yayin karbar bakoncin Yarima mai jiran gado na Saudiya Mohammed bin Salman a fadar Elysée. © Bertrand Guay / AFP
Talla

Amnesty wadda ta yi amfani da damar ziyarar da yariman na Saudiya ke yi yanzu haka a Faransa, ta ce galibin samarin mabiya akidar shi’a ne marasa rinjaye da ke ta Saudiya kuma sun aikata laifukan da ake tuhumarsu ne tun gabanin shekarunsu ya kai na iya gurfana gaban kotu.

Karkashin dokokin Saudiya janye hukunci bayan zartas da shi musamman a abin da ya shafi aqida lamari ne mai cike da sarkakiya wanda ya sanya tunanin ganin cewa abu ne mai matukar wahala kiran ya yi tasiri. 

Masu fafutuka na son Macron ya jaddada muhimmancin kare hakkin bil adama yayin ganawarsa da Yarima Mohamed bin Salman a yau Juma’a, wanda har yanzu ke fuskantar suka kan kisan gillar da aka yi wa dan jarida Jamal Khashoggi cikin shekarar 2018 a ofishin jakadancin Saudiya da ke birnin Istanbul na Turkiya. 

Wannan ce ziyarar farko da yariman na Saudiya da ake yiwa lakabi da MBS ke kaiwa Faransa tun bayan zarginsa da kisan kai wanda ya sanya kungiyoyin kare hakkin dan adam mika bukatar kamenshi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.