Isa ga babban shafi

Hare-hare sun fara dawowa a Sudan ta kudu gabanin babban zaben kasar

Hukumomin Sudan ta Kudu sun tabbatar da mutuwar akalla mutane 12 da aka bindige har lahira, yayin da wasu yara 15 suka yi batan dabo bayan da wasu fusatattun matasa suka farmaki wani kauye da ke yankin gabashin kasar.

Біженці із Західного Дарфуру у Чаді, липень 2023
Wani yanki a Sudan ta Kudu. © Zohra Bensembra / Reuters
Talla

Wannan hari na fusatattun matasan na zuwa ne a dai-dai lokacin da rigingimun cikin gida ke ci gaba da zafafa harkokin siyasa gabanin zaben kasar.

Ministan yada labaran yankin Abraham Kelang, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce harin ya afku ne a ranar Lahadin da ta gabata lokacin da matasan suka farmaki kauyen Ajwara da ke gundumar Pochalla.

Irin wannan dai ya saba faruwa a yankin na Boma, ko da a karshen watan Maris din da ya gabata ma sai da wasu matasa suka harbe mutum 15 har lahira ciki har da mataimakin kwamandan sojojin yankin da wasu jami’an gwamnatin kasar ta Sudan ta Kudu.

Sudan ta Kudu dai na fama rikice-rikicen kabilanci tun daga shekarar 2013 har zuwa 2018, lamarin da ya haddasa mutuwar dubban al’ummar kasar, har kawo yanzu kuma kasar na ci gaba da fuskantar rikice-rikice tsakanin masu dauke da makamai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.