Sudan ta zama kasa mafi yunwa a tarihi bayan yakin watanni 11- MDD
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa Sudan na shirin zama kasa mafi yunwa a Duniya sakamakon yakin kusan shekara guda da aka shafe ana gwabzawa tsakanin dakarun kai daukin gaggawa na RSF da Sojin kasar.
Wallafawa ranar:
Kwamitin tsaro na majalisar wanda ya bukaci tsagaita wuta a wannan yaki na watanni 11 tun gabanin kamawar watan Ramadana, yanzu haka akwai mutum miliyan 18 da ke matsayin kashi 2 bisa 3 na al’ummar kasar da ke fama da matsananciyar yunwa.
A cewar rahoton kwamitin, tuni yakin ya jefa miliyoyin kananan yara a halin matsananciyar yunwa saboda karancin abinci wanda har ya kai ga asarar rayukan wasun su.
Rahoton ya ce matsalar ta fi tsananta a yankin Oundurman da yakin ya ta'azzara miliyoyin al'umma ta yadda aka samu rahotannin kisan kananan yara da kuma yi wa mata fyade.
A cewar Rahoton dole ne a samar da mafita ga miliyoyin al'ummar kasar tun gabanin matsalar ta yunwa ta karade sassan kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu