Isa ga babban shafi

Yunwa za ta illata kashi 1 bisa 3 na al'ummar Sudan - MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin yiwuwar kashi 2 bisa 3 na al’ummar Sudan su fuskantar matsananciyar yunwa a kaka mai zuwa sakamakon yakin tsawon watanni da kasar ta yi fama da shi wanda ya kassara tsarin samar da abinci.

Wasu mutane da ke girki a wata makaranta da aka mayar mafakar 'yan gudun hijirar Sudan a garin Wadi da ke Arewacin Sudan mai iyaka da Masar, ranar 11 ga watan Satumba, 2023.
Wasu mutane da ke girki a wata makaranta da aka mayar mafakar 'yan gudun hijirar Sudan a garin Wadi da ke Arewacin Sudan mai iyaka da Masar, ranar 11 ga watan Satumba, 2023. © AFP - ASHRAF SHAZLY
Talla

Rahoton wanda Majalisar ta fitar a jiya Alhamis, ya bayyana cewa akwai akalla mutane miliyan 30 da za su yi fama da matsananciyar yunwa a Sudan adadin da ke wakiltar kashi 1 bisa 3 na al’ummar kasar, lamarin da ke na da sabada da yakin da ya barke tun a tsakiyar watan Aprilu tsakanin dakarun kai daukin gaggawa na RSF da sojin kasar.

Majalisar ta ce yanzu haka miliyoyin jama’a a Sudan sun sauya tsarin cin abincinsu zuwa sau daya a rana maimakon 3 wanda ke nuna matukar ba a kawo karshen yakin kasar ba, karin mutanen da za su fuskanci yunwa ka iya karuwa, lura da karancin abinci da kuma rashin damar shigar da kayakin agaji yankunan da suka kamata.

Shugaban shirin abinci na Majalisar, Eddie Rowe ya ce a yanzu haka rabin al’ummar birnin Khartoum na tsananin bukatar agajin gaggawa kari kan wasu mutum miliyan 18 da hukumar IPC ke cewa suna tsananin bukatar agajin baya ga yankunan Darfur da Kordafan wadanda lamarin yafi tsananta.

A cewar IPC nan da watan Mayun badi, matukar ba a dauki matakan da suka kamata ba, yunwar za ta lahanta iyalai da dama lura da yadda za a fuskanci mafi munin karancin abinci.

Yanzu haka dai Sojojin Sudan sun sanya shingaye a wasu yankuna irinsu al-Shajara yayinda RSF ke kawar da duk wani tallafi da ya nufi yankunan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.