Isa ga babban shafi
RIKICIN SUDAN

An dakatar da tattaunawar neman kawo karshen yakin basasar kasarSudan a kasar Saudiya.

Masu shiga tsakani na kasashen Saudiyya, Amurka da Afirka sun dakatar da tattaunawar da ake yi tsakanin sojojin Sudan da dakarun rundunar kai daukin gaggawa ta RSF a birnin Jeddah  na Saudiyya.An dakatar da tattaunawar ne saboda gaza cika alkawuran da suka dauka na aiwatar da matakan karfafa kwarin gwiwa, da kuma janye dakarun soji daga muhimman garuruwa, a cewar kafafen yada labaran Sudan.

Abdelfattah Al-Burhan ; Shugaban Rundunar Sojin Sudan  da t Mohamed Hamdan Dogolo, da ake kira "Hemedti" ; comandan dakarun rundunar kai daukin gaggawa ta RSF
Abdelfattah Al-Burhan ; Shugaban Rundunar Sojin Sudan da t Mohamed Hamdan Dogolo, da ake kira "Hemedti" ; comandan dakarun rundunar kai daukin gaggawa ta RSF © Monicah Mwangi-Reuters - Ashraf Shazly-AFP
Talla

Duk da cewa, masu jagorantar tattaunawar hadin gwiwa ta Tarayyar Afirka da Amurka da Saudiyya ba ta sanar da dakatar da tattaunawar ba a hukumance, amma har yanzu ba a kai ga cimma matasaya ba.

A ranar 7 ga watan Nuwamba, bangarorin biyu sun cimma yarjejeniya da ke bayyana matakan saukaka ayyukan jin kai ga fararen hula, har ila yau sun amince da aiwatar da matakan karfafa gwiwa, musamman da za su ba da damar kame tsoffin shugabannin gwamnatin da suka tsere daga gidan yari, da suka hada da manyan jagororin hambararren gwamnatin Omar al-Bashir da suka tsere daga wuraren da ake tsare da su tun farkon watan Disambar bara.

An kaddamar da yakin  a ranar 15 ga watan Afrilun da ya gabata tsakanin sojojin Sudan karkashin jagorancin Janar Abdel Fattah al-Burhane, da kuma dakarun Rapid Support Forces (RSF) na Janar Mohamed Hamdane Daglo, ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 9,000 tare da raba sama da miliyan 6 da muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.