Isa ga babban shafi

Masu rikici a Sudan ba su da niyyar sasantawa

Sojojin Sudan da mayakan sa-kai na RSF da suka shafe tsawon watanni takwas suna rikici da juna, sun bayyana shakku game da wata sanarwa da masu shiga tsakani suka fitar wadda ke cewa, bangarorin biyu sun amince da tsagaita musayar wuta da kuma tattaunawar siyasa a tsakaninsu.

Janar  Abdel Fattah al-Burhan da janar Mohamed Hamdan Daglo.
Janar Abdel Fattah al-Burhan da janar Mohamed Hamdan Daglo. © AP
Talla

Kungiyar Kasashen Gabashin Afrika, IGAD tare da taimakon Amurka da Saudiya, ta bukaci shiga tsakani domin kawo karshen yakin na Sudan da ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da dubu 12, baya ga fiye da miliyan 6 da dubu 5 da suka rasa muhallansu, yayin da kuma rikcin ya yi lagaga da tattali arzikin kasar.

A jiya Lahadi ne kungiyar IGAD ta bayyana cewa, shugaban mulkin sojin Sudan, Janar Abdel Fattah al-Burhan da jagoran dakarun sa-kai na RSF, Mohamed Hamdan Dagalo sun amince su gudanar da wani zama irinsa na farko tun bayan barkewar rikicin tare da gabatar da kudirin tsagaita musayar wuta.

Sai dai gwamnatin sojin Sudan ta bakin ma’aikatar harkokin wajenta ta ce, ko kadan ba ta da masaniya game da sanarwar da IGAD ta fitar, tana mai cewa, koda kuwa za ta zauna da Dagalo don  kulla yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta din-din-din da kuma janyewar RSF daga birnin Khartoum, to lallai akwai wasu sharudda da sai an fara mutunta su.

Ita RSF ta ce, tana da nata sharuddan kafin zaman tattaunawar da suka hada da cewa, ba ta amince da Janar Burhan a matsayin shugaban mulkin soji ba, yayin da ake ganin cewa, babu shakka, gwamnatin sojin Sudan ba za ta amince da wannan sharadin ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.