Isa ga babban shafi

Hatsarin jirgin sama ya kashe mutum bakwai a Burkina Faso

Wani hadarin karamin jirgi a Burkina Faso yayi sanadin mutuwar mutane 5 cikin guda 7 da ke cikin jirgin.

Jami'an agaji da sauran mutane a wurin da jirgin sojin saman Najeriya ya fadi yayin kokarin sauka a filin jiragen sama na birnin Abuja.  21/2/ 2021.
Jami'an agaji da sauran mutane a wurin da jirgin sojin saman Najeriya ya fadi yayin kokarin sauka a filin jiragen sama na birnin Abuja. 21/2/ 2021. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Bayanai sun ce jirgin ya yi karo da bishiya a lokacin da yake kokarin tashi a gabashin kasar, kuma mutane biyun da basu rasa ransu ba sun gamu da mummunan rauni.

Jirgin mai zaman kansa na yunkurin tashi ne daga filin jirgin saman Diapaga zuwa garin Fada N’Gourma, kamar yadda kamfanin dillanci labaran kasar ya tabbatar.

Faya-fayan bidiyo sun nuna yadda jirgin ya kone kurmus, bayan da wuta ta tashi jim kadan bayan faduwar sa.

Har yanzu dai babu cikakken bayani game da dalilin faduwar jirgin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.